Sifeton Janar na yan sanda ya karawa jami’an da suka damke mai garkuwa da mutane ‘Evans’ girma

Sifeton Janar na yan sanda ya karawa jami’an da suka damke mai garkuwa da mutane ‘Evans’ girma

- Sifeto Janar na hukumar yan sanda, Ibrahim Idris, ya karawa yan sanda girma bisa ga kyawun aikinsu

- An kara musu girma domin karfafa musu guiwa akan cigaba da aiki

- Sune suka taimaka wajen damke babban mai garkuwa da mutane Duneme Onwuamadike wanda akafi sani da Evans.

Wata rahoton Daily Sun ta nuna cewa sifeto janar na hukumar yansandan Najeriya, IGP Ibrahim Idris, ya amince da karawa jami’an yan sandan da suka bada gudunmuwa wajen damke babban mai garkuwa da mutane, Duneme Onwuamadike wanda akafi sani da Evans.

Sifeton Janar na yan sanda ya karawa jami’an da suka damke mai garkuwa da mutane ‘Evans’ girma

Sifeton Janar na yan sanda ya karawa jami’an da suka damke mai garkuwa da mutane ‘Evans’ girma

Game da cewan rahoton, IGP ya yanke shawaran hakan ne domin karfafa musu guiwa bayan fadar shugaban kasa ta yabeshi kan aikin.

KU KARANTA: Yan majalisan da suka fi dadewa a majalisa

Wata majiya tace jami’an yan sanda 46 ne suka kai harin.

An karawa Sajen 29 girma zuwa matsayin Sifeto, yayinda aka karawa Kofura 3 girma zuwa matsayin Sajen.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naij.com

Related news
Babbar magana: An sace wasu Turawa 4 a Najeriya

Babbar magana: An sace wasu Turawa 4 a Najeriya

Babbar magana: An sace wasu Turawa 4 a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel