Assha: Ministan Najeriya ya cirewa Shugaba Buhari zani a kasuwa

Assha: Ministan Najeriya ya cirewa Shugaba Buhari zani a kasuwa

– Ministan kwadago Sanata Ngige yayi magana game da Gwamnatin Buhari

– Chris Ngige ya bayyana abin da ya sa Gwamnatin Buhari ta saba alkawari

– Gwamnatin Buhari tayi alkawarin samawa miliyoyin Jama’a aikin yi

Ministan Buhari yace matsalar tattali ya hana Shugaba Buhari cika alkawari

Shugaba Buhari yayi kamfen cewa zai samawa mutane miliyan uku aikin yi

Gwamnatin dai ta saba wajen cika wannan alkawari da tayi ga ‘yan kasar

Assha: Ministan Najeriya ya cirewa Shugaba Buhari zani a kasuwa

Wani Ministan Buhari yace Gwamnatin su ba ta cika alkawari ba

Ministan kwadago na Najeriya watau Sanata Chris Ngige ya bayyana abin da yasa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta saba alkawarin da tayi wa ‘Yan Najeriya a baya na samawa mutane har miliyan uku aiki a kowace shekara.

KU KARANTA: Yadda Dangote ya hana a tsige Sarki Sanusi II

Assha: Ministan Najeriya ya cirewa Shugaba Buhari zani a kasuwa

Ministan Kwadago na Najeriya Ngige

Ngige ya bayyana cewa Gwamnatin Buhari ta samu kasar cikin mugun matsi ne na tattalin arziki wanda hakan ya hana a cika alkawarin da aka yi wa ‘Yan kasar shekaru 2 da su ka wuce.Ngige yace cin hanci ya dabaibaye komai a harkar kasar.

Kwanaki Ministan yake cewa da bakin sa Jama’an Najeriya da dama sun yi burin ganin canji fiye da haka daga Gwamnatin su sai dai yace duk da haka shi yana jin cewa wannan Gwamnati tayi matukar kokari.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Tsohon gwamna yayi ma wata mata data haifi ýan 4 ruwan alheri a Sakkwato (Hotuna)

Tsohon gwamna yayi ma wata mata data haifi ýan 4 ruwan alheri a Sakkwato (Hotuna)

Wata mata ta fara cin albarkar haihuwa ýan 4, wani Sanata yayi mata alheri rututu (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel