Wasanni: Za'a rage lokacin wasan kwallon kafa zuwa mintuna 60 kacal

Wasanni: Za'a rage lokacin wasan kwallon kafa zuwa mintuna 60 kacal

- Ana shirin kawo wasu sauye-sauye a wasan kwallon kafa ciki har da rage lokacin wasan ya zama minti 60, inda za a rika tafiya hutu bayan minti 30.

- Majalisar da ke dokokin wasan ta duniya (ifab) ta ce tana son kawo wannan sauyi ne saboda kusan minti 60 kawai ake yi na tsagwaron wasa a cikin minti 90, sauran lokacin duk kusan dabaru ne na bata lokaci da 'yan wasa kan yi.

Wani sauyin da ake shirin kawowa kuma shi ne, a duk lokacin da dan wasa ya buga fanareti ba ta shiga ba ta dawo, babu damar a sake bugawa, an yi asararta.

Sauran shawarwarin su ne hada agogon filin wasan ya zama yana aiki daidai da agogon alkalin wasa, sannan da wata sabuwar doka da za ta ba dan wasa dama ya ba wa kansa da kansa kwallo a lokacin da zai yi bugun tazara.

Wasanni: Za'a rage lokacin wasan kwallon kafa zuwa mintuna 60 kacal

Wasanni: Za'a rage lokacin wasan kwallon kafa zuwa mintuna 60 kacal

NAIJ.com ta samu labarin cewa tsohon dan wasan Chelsea na gaba Gianfranco Zola yana goyon bayan rage lokacin wasan daga minti 90 zuwa 60, saboda ya ce yana ganin akwai kungiyoyi da dama da ke bata lokaci su ki tsayawa su yi wasa idan suna kan gaba.

Shi ma mai tsaron ragar Arsenal Petr Cech ya goyi da bayan Zola inda ya bayyana cewa a yanzu kusan minti 25 ne kawai ake yi a kowane kashi daya na wasan, saboda haka idan aka rage lokacin za a riga ganin tsagwaron wasa ne kawai.

Ifab ta kunshi hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, da hukumomin kwallon kafa na yankuna hudu na Birtaniya - Ingila da Scotland da Wales da Ireland ta Arewa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
An kama wani sojan da ya gudu daga yaki da Boko Haram da laifin sata

An kama wani sojan da ya gudu daga yaki da Boko Haram da laifin sata

Wani sojan da ya gudu daga yaki da Boko Haram ya shiga hannu jami'an tsaro
NAIJ.com
Mailfire view pixel