365

USD/NGN

Mutane 88 su ka mutu a hatsarin mota a jihar Bauchi – Hukumar kula da hadura

Mutane 88 su ka mutu a hatsarin mota a jihar Bauchi – Hukumar kula da hadura

- Akalla mutane 88 suka rasa rayukan su yayin da 572 sun jikkata a hatsararruka daban daban a jihar Bauchi tsakanin watan Janairu zuwa Mayu 2017

- An samu wannan bayanin ne a cikin rahoton hatsararruka da Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi ta fitar.

Rahotan ya nuna cewa mutane 1,364 hatsararrukan ya shafa a hatsarin mota, hatsararruka 24 daga cikin hatssarin sun zama mummunan abu, yayin da 79 daga ciki hatsari masu tsanani, inda 23 a cikin hatsararrukan kananan hatsari ne saboda babu wadanda suka rasa rayukan su.

NAIJ.com ta samu labarin cewa kwamandar hukumar na yankin, Abdulrazak Najume, ya hatsararruka sun karu a jihar saboda yawan gudu da mota ba a bisa doka ba sannan kuma da gyaran hanyar titi da ake yi a cikin jahar Bauchi da wajen jahar tare da cire dan tudun da ake yi a kan hanya don rage gudun mota (kabarin mai-tsane) a manya hanyoyi.

Ya ce cire kabarurrukan mai-tatsane da aka yi ya sa mutane na gudu a bisa kan hanya. “Yawan irin wannan ganganci ya sa mutane cikin damuwa, tare da irin hatsararrukan da ke guduna a fadin jahar a manya tituna fa kanana a birnin jahar. Da kamar wuya a rana ba a samu jami’an mu sun fita ceto mutane da hadari ya shafa ba. Duk da cewa a kullun muna wayar da kan mutane a kullun game da illolin guje guje a kan bisa kan hanya, amma mutane ba su ji.” Ya ce.

Related news
Yadda ýan bindiga daɗi suka diran ma hukuma EFCC da safiyar Laraba, suka kai hari (Hotuna)

Yadda ýan bindiga daɗi suka diran ma hukuma EFCC da safiyar Laraba, suka kai hari (Hotuna)

Da ɗumi ɗumi: ýan bindiga sun kai hari hedikwatar EFCC, sun bar babban jami’in hukumar saƙo
NAIJ.com
Mailfire view pixel