Mulkin farar hula ake yi a Najeriya ba dimokradiyya ba - Tinubu

Mulkin farar hula ake yi a Najeriya ba dimokradiyya ba - Tinubu

- Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC ) Bola Tinubu ya bayyana cewa Najeriya bata fara gudanar da tsarin mulkin demokradiyya ba

- Tinubu ya ce damokradiyyan da ake tafiyarwa a Najeriya baza’a iya kiransa da cikakken demokradiyya ba

- Shugaban jam’iyyar ta APC ya ce har yanzu ana kokari don ganin an fara demokradiyya

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma babban jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba a gudanar da tsarin mulkin dimokradiyya a Najeriya ana dai mulkin farar hula ne.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayinda ya ke karbar kanbin da mujallar Tell ta ba shi a matsayin Jagoran Dimokradiyya na shekara.

KU KARANTA KUMA: Najeriya daya! Hausawa sunyi shiga irin ta ‘yan kabilar Igbo don nuna kauna, bayan barazanar Arewa

Mulkin farar hula ake yi a Najeriya ba dimokradiyya ba - Tinubu
Mulkin farar hula ake yi a Najeriya ba dimokradiyya ba - Tinubu

Tinubu da ya samu wakilcin tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Legas, Dele Alake ya ce: “Wannan mulki na farar hula da ake yi a Najeriya ba za a iya kiransa da tsarin Dimokradiyya kai tsaye ba.

“Tsarin dimokradiyya a Najeriya za a iya cewa abu ne da zai faru a nan gaba da yardar Allah tunda dai ana tafiya ne akan mulkin farar hula.

“A saboda haka ne na ke jan hankalinmu da mu hada kai da fata wajen ganin cewa mun tabbatar da tsarin dimokradiyya a Najeriya tunda dai mun san ginshikansa, mun san tanade-tanadensa. Da fatan za mu kai ga cimma wannan tsari a lokacin rayuwarmu.”

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel