• 362

    USD/NGN

Farfesa Osinbajo ya yi sabbin nade-nade

Farfesa Osinbajo ya yi sabbin nade-nade

- Ana zargin Osinbajo da bangaranci wurin nade-nade

- An nada Abdurrahman Baffa Yola a mukami

- Osinbajo na kara samun gindin zama a matsayin shugaba

A ci gaba da tafiyar da mulki yadda zai fi yi masa dadi, mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, na ci gaba da nade-nade na wadanda zasu taimaka masa iyar da ragamar mulki, da ma kuma gurabe wadanda duk tsawon shekarun mulkin Buhari, ba'a cike ba, tun bayan na PDP.

Sai dai, a yanzu, an dan sami chanji, inda aka shugaban ya fara nada musulmai 'yan arewa, bayan zarge-zarge da ake masa da nada asalin 'yan kabilarsa a fadar mulki, da ma wai yan bangaren kudu.

Farfesa Osinbajo yayi sabbin nade-nade

Farfesa Osinbajo yayi sabbin nade-nade

A yau an sami nada Alh. Abdurrahman Yola a matsayin hadimin shugaban kasa kan harkokin gwamnati, wato intergovernment affairs.

Makusantan Abdurrahman din dai sunce ya dade yana bautawa jam'iyyarsa ta APC, kuma lallai ya cancanta a matsayin da aka bashi.

Ana zuba ido dai a ga irin sauran nade-nade da shugaba Osinbajo zayyi a mako mai zuwa. Sai ku biyomu:

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Related news

Ka ga wanda Dan wasan kwaikwayo Zaharaddeen Sani ya kai wa ziyara kuwa?

Ka ga wanda Dan wasan kwaikwayo Zaharaddeen Sani ya kai wa ziyara kuwa?

Fitaccen Dan wasan Hausa ya kai wa babban Jami'in 'Yan Sanda ziyara
NAIJ.com
Mailfire view pixel