Garabasa: Sunnah 10 na Manzon Allah SAW a Ranar Idi

Garabasa: Sunnah 10 na Manzon Allah SAW a Ranar Idi

– Musulmai na shirin murnar karamar Sallah a Duniya

– Da zarar Azumi ya kare za ayi biki a Duniyar Musulmai

– Akwai sunnoni da dama a wannan rana da ya kamata a kiyaye

Garabasa: Sunnah 10 na Manzon Allah SAW a Ranar Idi

Bikin Sallah: Sarkin Musulmi a Ranar Idi

NAIJ.com ta kawo maku wasu sunnonin Manzon Allah a matsayin garabasar wannan shekara.

1. Wankan tsarki

Ana bukatar wankan gusul kafin a je Masallacin Idi

2. Karin safe

Yana cikin sunnah a samu wani abinci a tauna kafin a tafi Masallacin Idi a lokacin karamar Sallah.

3. Sababbin kaya

Daga cikin Sunnah ana so a sanya sababbin kaya a Ranar Sallah ko kuma mafi kyau akalla

4. Sallar Nafila

Bai halatta ayi Sallar Nafila a filin Idi ba yayin da ake jirar Liman.

KU KARANTA: Ashe Darika da Shi'a duk daya ne- Inji Babban Shehi

5. Nafila a gida

Ana kuma so ayi nafila raka’a 2 rak yayin da aka dawo daga Masallacin Idi watau a gida.

6. Sauya hanya

Yana daga cikin Sunnah a canza hanyar da aka bi wajen zuwa yayin da ake dawowa gida

7. Takawa a kafa

An so a je Masallaci a kafa ba bisa wani abin hawa ba domin zuwa Sallar Idi.

8. Gaisuwa

Sahabbai kan gaida ‘Yan uwan su yayin da su ka hadu domin murna a wannan rana.

9. Ziyara

Ziyarar ‘Yan uwa da abokan arziki na cikin Sunnah a wannan lokaci na farin ciki.

10. Kabarbari

Ana fadan Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ilaha illalLah, Allahu Akbar, Wa lilLahil hamd.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jama'a na fadin albarkacin bakin su game da Evans

Source: Hausa.naij.com

Related news
Wani sabon rikici zai kaure tsakanin Sanatoci da Shugaba Buhari

Wani sabon rikici zai kaure tsakanin Sanatoci da Shugaba Buhari

Wani sabon rikici zai kaure tsakanin Sanatoci da Shugaba Buhari
NAIJ.com
Mailfire view pixel