Mata 5 sun rasa rayukansu a wajen turmutsutsun karbar kakkar Naira 500 a Katsina

Mata 5 sun rasa rayukansu a wajen turmutsutsun karbar kakkar Naira 500 a Katsina

- Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukan su wajen karbar zakkar Naira dari biyar biyar a jahar Katsina.

- Wadanda suka rasa rayukan na su sun kunshi kananan yara guda 4 da wata mata mai kimanin shekaru 40.

Wannan mummunan sha’ani ya faru ne yayin da darururuwan mutane suka taru a gidan mutumin da ke raba zakkar mai suna Kamal Ma’a Gafai, a yankin Rafin Dadi da ke jahar.

Mata 5 sun rasa rayukansu a wajen turmutsutsun karbar kakkar Naira 500 a Katsina

Mata 5 sun rasa rayukansu a wajen turmutsutsun karbar kakkar Naira 500 a Katsina

NAIJ.com ta samu labarin cewa mai magana da yawun ‘yan sandan jahar DSP Gambo Isah ya shaidawa manema labarai cewa banda wadanda suka rasu, akalla mutane 15 sun jikkata.

Ya ce an kai mutane 15 din asibiti inda aka yi masu magani aka kuma sallame su.

Shi kuwa Gafai mai raba Zakka, DSP Isah ya ce yanzu haka ya na hannun su kuma sun shiga bincike akan shi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Labari da duminsa: Sanata Misau ya gurfana gaban kotu bisa zargin da ya jefa kan Sifeta Janar na 'yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel