Kungiyar Izala ta raba kayan tallafi ga marayu 2,000 a jihar Adamawa (Hotuna)

Kungiyar Izala ta raba kayan tallafi ga marayu 2,000 a jihar Adamawa (Hotuna)

- Kungiyar Izala reshen jihar Adamawa ta raba kayan tallafi ga wasu marayu 2,000 a jihar

- Shugaban kwamitin marayu ta kungiyar ya ce kwamitin na raba kayan tallafi makamancin wannan kowace shekara

- Sheikh Dakta Abdulqadir Saleh Kazaure ya yi wa’azi cewa falalan dake cikin tallafawa marayu yana da yawa sosai

A ranar Laraba, 21 ga watan Yuni ne kungiyar Jama'atul Izalatil Bidi'ah Wa Ikamatis Sunnah reshen jihar Adamawa ta kaddamar da raba kayan tallafi ga marayu 2,000 a fadin jihar.

Alh. Usman Ibrahim shine shugaban kwamitin marayun a jihar Adamawa kuma sakataren kwamitin a matakin kasa, a yayin da yake jawabi a wurin kaddamar da tallafin yace a wannan shekara an tantance marayu 2,000 ne a wannan shekarar. Ya ce kamar yanda aka saba, kowani azumi kwamitin tasu ta marayu tana raba kayan tallafi makamancin wannan kowace shekara.

A yayin da yake jawabi, shugaban kungiyar Izala ta jihar Adamawa Alh. Sahabo Magaji ya jinjina wa kwamitin na marayu, inda ya ce taimakawa marayu na daya daga cikin manyan ayyukan kungiyar. Shugaba Sahabo ya yi godiya ga jama'a bisa hadin kai da suka bada ta hanyar bada taimakon su.

Kungiyar Izala ta raba kayan tallafi ga marayu 2,000 a jihar Adamawa (Hotuna)

kayan tallafin da kungiyar Izala ta raba wa marayu 2,000 a jihar Adamawa

KU KARANTA: Bayan Pogba, dubi dan kwallon daya je aikin Umara a Saudiyya kuma

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Sheikh Dakta Abdulqadir Saleh Kazaure, malamin da kungiyar ta turo tafsiri a jihar Adamawa ya yi jawabi ne akan falalan dake cikin tallafawa marayu. Shehin malamin ya ce falala dake ciki yana da yawa sosai, musamman idan akayi la'akari da hadisin da yace Manzon Allah zai yi tarayya da mai taimakawa maraya a gidan Aljannah.

Kungiyar Izala ta raba kayan tallafi ga marayu 2,000 a jihar Adamawa (Hotuna)

Shugabanin kungiyar Izala reshen jihar Adamawa

Kungiyar Izala ta raba kayan tallafi ga marayu 2,000 a jihar Adamawa (Hotuna)

Mata ma halartar taron

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku saurari tsohon direban Bishof David Abioye na Living Faith Church wanda ya karbi musulunci bayan ficewa daga cocin

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel