An kai karar sarauniyar Ingila ga 'yansanda

An kai karar sarauniyar Ingila ga 'yansanda

- 'Yan sanda sun Sami rahoto akan Sarauniyar Ingila

- Tsegumi akan Sarauniyar Ingila ta lambar kar-ta-kwana ta 999

- A daina Kiran layin 999 idan ba matsala ta gagawa bane - Tom Donohoe

Rundunar 'yan sandan West Yorkshires' da ke Ingila sun bada sanarwa ta shafin sada zumunta na twitter cewa wani mutum ya kira layin kar-ta-kwana na 999 ya tsegunta masu cewa Sarauniyar Ingilan bata sa bel ba a motar da ake tuka ta a London a hanyar zuwa bukin bude zaman Majalisa. Tare da Sarauniyar akwai Yarima Charles a cikin motar.

An kai karar sarauniyar Ingila ga 'yansanda

An kai karar sarauniyar Ingila ga 'yansanda

Duk da wannan rahoton, baza a iya tuhumar Sarauniyar ba domin dokar kasar ta Ingila ya Sarauniyar kariya na musamman daga irin wadannan laifufukan.

Ofishin yada labarai na fadar Saurauniyar yace bazai yi tsokaci akan wannan labarin ba.

Tom Donohoe na rundunar 'yan sandan West Yorkshire yace sau da yawa mutane suna kiran layin kar-ta-kwana ta 999 amma ba dalilan kiran nasu ba matsala bace ta gagawa.

"Muna kara tunatar da jama'a lambar 999 ana kiran ta ne kawai domin matsala ga gagawa" Inji Donohoe

Ya cigaba da cewa rundunar tana samun kira sama da 1000 a lambar ta 999 a kowane rana.

A kwanakin baya rundunar ta taba wallafa rahoto akan irin kiraye-kirayen da take samu a lambar 999 din, cikin su harda wanda suka kira domin su bada rahoton cewa bera yana musu shige da fice a gida.

Game da sanya bel a mota kuwa, doka ta tilasta wa kowa yayi amfani da bel din matukar akwai ta a motan. Rashin yin bin dokan yana iya sa aci mutum tara har na fam 500. An yi rangwanci akan direbobin motocin 'yan sanda da masu kashe gobara da direban da ke tafiya baya da baya.

Daga karshe, Shafin masarautan Ingila yace "Sarauniyar tana taka tsantsan wajen gudunar da harkokin ta bisa ga tsarin dokan

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel