366

USD/NGN

EFCC: An tasa tsohuwar Ministar mai Diezani a gaba

EFCC: An tasa tsohuwar Ministar mai Diezani a gaba

– Kotu ta ba Hukumar EFCC ta cigaba da bankado shaida kan Diezani Madukwe

– Ana zargin tsohuwar Ministar man da satar kudin al’umma lokacin tana ofis

– Hukumar EFCC na karar tsohuwar Ministar da wasu mutanen dabam

Babban Kotun Tarayya ta ba EFCC dama a kan Ministan mai Diezani. Kotu ta ba Hukumar EFCC dama tayi ta bankado shaida kan laifin ta. Ana zargin tsohuwar Minista Diezani Alison-Madukwe da laifuffuka rututu.

EFCC: An tasa tsohuwar Ministar mai Diezani a gaba

Ana zargin Diezani Alison-Madukwe da laifin sata

Babban Kotun Tarayya da ke Birnin Tarayya ta ba Hukumar EFCC mai yaki da zamba dama ta cigaba da bankado duk wata shaida a kan tsohuwar Ministar mai Diezani Alison-Madukwe da ake zargi da laifin sata.

KU KARANTA: An maka karara Sarauniya wajen 'Yan Sanda

EFCC: An tasa tsohuwar Ministar mai Diezani a gaba

EFCC na zargin tsohuwar Minista Diezani da laifuffuka 9

Ana zargin tsohuwar Ministar man da laifuffuka har 9 wanda daga ciki akwai satar kudin al’umma lokacin tana Ministar harkokin man fetur a lokacin shugaba Jonathan. Har da wasu yaran na ta Hukumar ta ke kara a halin yanzu.

Wasu dai na ganin cewa Gwamnatin Buhari ta tasa mutanen Jonathan a gaba ko shekaran jiya wancan Hukumar EFCC ta gayyaci wata tsohuwar Ministar Najeriya Stella Oduah bisa zargin kashe sama da Naira Miliyan 255 wajen sayen manyan motoci.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Me ya dace ayi da Evans; mai garkuwa da mutane

Related news
Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe

Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe

Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe
NAIJ.com
Mailfire view pixel