Dandalin Kannywood: Shararriyar jaruma Maryam Booth ta rabawa marayu kayan sallah

Dandalin Kannywood: Shararriyar jaruma Maryam Booth ta rabawa marayu kayan sallah

- Jaruma Maryam Booth tayi rabon kayan sallah ga marayu kananun yara maza da mata a Nasarawa dake kano.

- Jarumar ta raba shaddoji da yadika masu din ki da ado na zamani.

NAIJ.com ta samu labarin cewa awajen rabon ne wakiliyar majiyar mu Maryam Hotoro ta sami sukunin zantawa da jarumar kamar haka:

Maryam kin rabawa marayu kayan sawa, kuma da alamu wadan nan yara marayune, wanne hange ki kayi wanda yasa ki ka rabawa marayu kayan sallah amadadin ki ba masu iyaye?

Wannan tambaya tana da saukin amsawa. Domin amsarta yana cikin tambayarki. Duk yaron yake da iyaye to tabbas yana da tabbacin samin kayan sallah, amma maraya bashi da tabbas. Dan haka naga gwara in ba marayu zaifi kyautuwa.

Dandalin Kannywood: Shararriyar jaruma Maryam Booth ta rabawa marayu kayan sallah

Dandalin Kannywood: Shararriyar jaruma Maryam Booth ta rabawa marayu kayan sallah

Me za kice da yan uwanki jarumai akan irin wannan abin alkairi da ki ki gudanar a yau?

Abinda zance shine, su ma Allah ya basu ikon gudanar da wannan abin alkairi. Duk da yake da yawan jarumai maza da mata suna irin wannan abin alkairin, nima da wasu nayi koyi irinsu A Zango, Sani Danja, Ali Nuhu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel