Gwamnatin tarayya ta shiga wata yarjejeniya da kasar Morocco don karya farashin shinkafa

Gwamnatin tarayya ta shiga wata yarjejeniya da kasar Morocco don karya farashin shinkafa

- Ministan dake lura da kasafin kudi da tsare-tsare, Udom Udoma yace gwamnatin tarayya tana aiki tukuru wajen ganin ta rage kudin takin zamani wanda haka zaisa farashin shinkafar da ake nomawa a gida yayi kasa.

- Ministan ya bayyana haka yayin da yake hira a gidan Talabijn kan kasafin kudin wannan shekara.

NAIJ.com ta samu labarin cewa yace don cimma wannan buri gwamnatin tarayya ta shiga yarjejeniya da kasar Morroco domin samar da sindarin Phosphate wanda muhimmi ne wurin hada takin zamani.

” Yawancin shinkafar da ake shigowa da ita kasarnan ana bawa manoman da suke nomata a kasashensu tallafi, hakan yana zama barazana ga shinkafar da ake nomawa a gida.

Gwamnatin tarayya ta shiga wata yarjejeniya da kasar Morocco don karya farashin shinkafa

Gwamnatin tarayya ta shiga wata yarjejeniya da kasar Morocco don karya farashin shinkafa

“matsalar anan itace ta rage kudin farashin shinkafar mu,muna kokari a wannan bangare ta hanyar samar da taki mai saukin kudi, saboda idan taki yayi tsada to abinci ma zaiyi tsada ,”yace

Udoma ya kara da cewa gwamnatin tarayya tana tallafawa manoma ta hanyar basu tallafin bashi mai sauki,karkashin shirin nan na babban bankin kasa, domin su kara yawan abinda suke nomawa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel