Mutane sama da 1,000,000 sukayi rejista a shafin Npower a cikin kwana 7

Mutane sama da 1,000,000 sukayi rejista a shafin Npower a cikin kwana 7

Akalla mutane Miliyan 1.1 masu digiri suka cike fom din samun aikin N-Power a cikin sati daya kacal da gwamnatin tarayya ta bude shafin yanar gizon samar da ayyuka na N-Power.

Babban mataimakin na musamman ga shugaban Buhari kan harkokin samar da ayyukan yi a kasa, Mr Afolabi Imuokhuede ne ya bayyana wannan a Asaba a lokacin da yake tattaunawa da wadanda suka samu nasarar samun aikin a shiri na farko a shekarar 2016.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Imoukhede ya gargadi wadanda suka samu aikin kuma suka ki zuwa aikin da cewa, gwamnati za ta maye gurbin su da wadanda ke neman aikin na N-Power a yankin.

Mutane sama da 1,000,000 sukayi rejista a shafin Npower a cikin kwana 7

Mutane sama da 1,000,000 sukayi rejista a shafin Npower a cikin kwana 7

Ya bayyana cewa, a shekarar 2016, akalla mutane 751,000 ne suka ci jarabawar da shirin N-Power ta gudanar wanda 300,000 daga cikinsu ba masu takardun digiri bane. Shirin ta samu daukar mutane 300,000 masu digiri inda a gaba za a fitar sunayen 300,000 marasa takardun digiri a watan Yuli na shekarar 2017.

Imoukhede ya ce wannan dai shafin da aka bude na shirin a yanzu na masu takardun digiri ne domin don cike adadin yawan wadanda ake son dauka.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Labari da duminsa: Sanata Misau ya gurfana gaban kotu bisa zargin da ya jefa kan Sifeta Janar na 'yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel