Kotu ta kawo wa Gwamna El-rufai matsala, ta dakatar da shirin sa na rusa masarautu 4,766 a Kaduna

Kotu ta kawo wa Gwamna El-rufai matsala, ta dakatar da shirin sa na rusa masarautu 4,766 a Kaduna

- Wata babbar kotu a garin Kafanchan, ta ba gwamnatin jihar Kaduna umarnin wucin-gadi, cewa ta dakatar da shirin ta na rushe Dagatai da hakimai dubu 4 a fadin jihar.

- Gwamnatin jihar Kaduna a karkashin jagorancin gwamna Nasiru El-Rufa’i, ta rushe Dagatai da Hakimai 4,776, bayan kwamitin sauya fasalin masarautu ya mika rahoton sa.

Kwamishinan masarautu da kananan hukumomi na jihar Kaduna Jafaru Sani, ya ce gwamnati ta dauki matakin ne domin rage yawan kudaden da majalisun kananan hukumomin ke kashewa.

Kotu ta kawo wa Gwamna El-rufai matsala, ta dakatar da shirin sa na rusa masarautu 4,766 a Kaduna

Kotu ta kawo wa Gwamna El-rufai matsala, ta dakatar da shirin sa na rusa masarautu 4,766 a Kaduna

NAIJ.com ta samu labarin cewa kotun dai, ta umarci gwamnati ta dakatar da shirin cike gibin, har zuwa lokacin da za a cigaba da sauraren shari’ar.

Mai shari’a S.S Daka ta dage shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Yuni na shekara ta 2017, bayan Stephen Gimba, da Gajere Dantawaye, da Ishaku Yari da Gambo Yaro sun shigar da kara a gaban kotun.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Labari da duminsa: Sanata Misau ya gurfana gaban kotu bisa zargin da ya jefa kan Sifeta Janar na 'yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel