YANZU YANZU: ‘Yan sanda sun kama Sojan da ke taimakawa mai garkuwa da mutane, Evans

YANZU YANZU: ‘Yan sanda sun kama Sojan da ke taimakawa mai garkuwa da mutane, Evans

- Rundunar ‘Yan sandan Najeriya sun kama wani jami’in soja dake taimaka wa gawurtaccen mai garkuwa da mutane, Evans

- An kama shi ne a Lagas

Rundunar ‘yan sanda sun kama wani soja a hukumar sojin Najeriya, Victor Chukwunonso, sakamakon samun shi da akayi da hannu dumu-dumu gurin taimaka wa babban mai garkuwa da mutanen nan, Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans.

Chukunonso dauke da lambar soji NO: 09/NA/64/6317 na daga cikin masu jami’an dake yi ma hukumar soji kida, a barikin Abatti, Surulere, Lagas.

KU KARANTA KUMA: Hotuna: Wani gurgu a garin Benue ya rungumi sana’ar kera takalma

Rahotanni sun kawo cewa jami’an sashin masu hikima na sufeto janar na ‘yan sanda ne suka kama shi a ranar Lahadi.

A halin yanzu NAIJ.com ta rahoto cewa gawurtaccen mai garkuwa da mutane Evans na hedkwatan yan sanda dake jihar Lagas, Ikeja, inda anan ne yake ta zayyana.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Labari da duminsa: Aminu Atiku Abubakar, da ga tsohon mataimakin Obasanjo, zai kwan a sijin, bisa wannan zargi, karanta

NAIJ.com
Mailfire view pixel