366

USD/NGN

'Yan bindiga sun halakar da mutane 4 a wani hari kan jami’an bincike a Kano

'Yan bindiga sun halakar da mutane 4 a wani hari kan jami’an bincike a Kano

- 'Yan bindiga a Kano sun halaka akalla mutane 4 a wani hari kan jami’an bincike

- Wani dan sanda da kuma mai gadi suka mutu nan take a harin

- ‘Yan bindigar sun yi awon gaba da bindigar dan sandan da suka kashe

Akalla mutane 4 ne aka kashe a daren ranar Asabar, 24 ga watan Yuni wato ranar jajiberin sallah a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta kan 'yan sanda a wani shingen bincike a kan hanyar Club Road da ke jihar Kano.

Wannan harin dai ya faru ne 'yan sa'o'i da fara shagulgular sallah na Eid-el-Fitr a jihar.

A cewar wasu mashaidi, wani dan sanda da kuma mai gadi a King’s Garden ne suka mutu nan take, yayin da kuma wani dan sanda ya ji rauni mai tsanani.

'Yan bindiga sun halakar da mutane 4 a wani hari kan jami’an bincike a Kano

'Yan bindiga sun halakar da mutane 4 a Kano

Rahotanni sun shaida cewa ‘yan bindigar wadanda ke kan babur, sun kwace bindigar dan sandan da suka kashe.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane 2, 000 ke garkame yanzu – IGP, Ibrahim Idris

NAIJ.com ta ruwaito cewa babu wata takamaiman bayani kan wannan harin daga rundunar ‘yan sandan jihar Kano har lokacin hada wannan rahoto.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya kamata a daure mai satar mutanen nan Evans ne ko gwamnati ta bashi aiki? Me nene ra'ayin ku masu karatu?

Related news
Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe

Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe

Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe
NAIJ.com
Mailfire view pixel