Dan tawaye Nnamdi Kanu ya yabi shuwagabannin arewa, ya soki Nnamdi Azzikiwe

Dan tawaye Nnamdi Kanu ya yabi shuwagabannin arewa, ya soki Nnamdi Azzikiwe

- Dan tawaye Nnamdi Kanu yayi tsokaci kan mazan jiya

- Ana zargin Nnamdi Kanu da kin jinin arewa, amma yace abun ba haka bane

- An san wasu daga kabilun Ibo da son kafa kasar Bayafara

A bayan zafafan kalamai na kabilanci da aka saba ji n shugaban kungiyar IPOB ta kabilar Ibo, Nnamdi Kanu, an jiyo shi a hira da 'yan jarida yana musanta yawan zarge-zarge da ake masa kan kin jini n kabilun hausa da arewa, inda yace ai shi yama fi son shuwagabannin arewa fiye da na kudu irin su Azzikiwe.

A cewar Nnnamdi Kanu, "ni ai nafi son ma shugaba Umaru Yar'aduwa da Alh. Shehu Shagari fiye da Nnamdi Azikiwe, saboda a lokacin Shehu Shagari ne na fara ganin manyan ayyuka daga jam'iyyar NPC."

A dai baya-bayan nan an jiyo wasu kabilun na arewa suna barazanar korar kabilar ibo ko kuma takura musu daga yankunan na arewa, wanda hakan zai iya zama shi Nnamdi Kanun ya jawo musu tsangwama kenan a arewa.

Dan tawaye Nnamdi Kanu ya yabi shuwagabannin arewa, ya soki Nnamdi Azzikiwe
Dan tawaye Nnamdi Kanu ya yabi shuwagabannin arewa, ya soki Nnamdi Azzikiwe

Ko a makon nan ma dai an jiyo Sanata Kwankwaso yana cewa watakil takara Nnamdi Kanun yake so a zabukan nan gaba.

Kanu din dai, ya kara da cewa, wasu tsiraru ne a arewar suke dakile ci gaba da son juna daga yankin, sun kuma hana sauran samarin yankin masu son juna fitowa su yada soyayya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel