Bangaren Shekau na Boko Haram ya fitar da sabon sakon Bidiyo

Bangaren Shekau na Boko Haram ya fitar da sabon sakon Bidiyo

- Shugaban Boko Haram yace zaman Najeriya bisa tsarin bature kafirci ne

- Shugaban yace bai kamata a zauna da kabilu ba tunda suma sahabbai wai basu yi ba

- Ya tabbatar da sace da bautar da mata da ya ce manyan yansanda ne

Bangaren tawaye na Boko Haram wanda 'yan ISIS na Syria suka tumbuke mulkin sa, suka nada wani yaronsa, bayan da yayi musu mubayi'a, ya sake fitar da wani sabon faifan bidiyo, wanda jaridar Sahara Reporters ta saki, inda ya tabbatar da bautar da satattun mata na 'yansanda.

Bangaren Shekau na Boko Haram ya fitar da sabon sakon Bidiyo

Bangaren Shekau na Boko Haram ya fitar da sabon sakon Bidiyo

A dai sabon bidiyon, Abubakar Shekau, wanda ya fito a ciki, ya yi kira ga sauran kabilun najeriya da su tuba su bi addininsa su bar Kafirci, domin wai, sahabbai basu zauna da kafirai a karkashin tsarin dagutu ba.

An nuna kuma tsofin faifan hare-hare na Boko haram a wasu yankunan.

Daga dukkan alamu dai a lokacin azumi aka nadi faifan, domin kalaman larabci a ciki na cewa watan azumi, watan juriya ne da yaki, da jihadi.

Ba'a dai ji daga bakin hukumar yan-sanda ba, ko sun tabbatar da sace jami'an nasu mata ko kuma a'a, labari wanda tun makon jiya NAIJ.COM ta kawo muku.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel