Atiku Abubakar ya jinjina ma muƙaddashin shugaban ƙasa Osinbajo

Atiku Abubakar ya jinjina ma muƙaddashin shugaban ƙasa Osinbajo

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jinjina ma Osinbajo

- Atiku yace yabon gwani ya zama dole

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yaba ma mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo sakamakon yadda yake tafiyar da mulkin kasar.

Atiku ya bayyana haka ne cikin sanarwar daya fitar na barka da Sallah ga musulman Najeriya, inda yace Osinbajo ya nuna kwarewarsa ta yadda ya tafiyar da kasar a wannan lokaci da wasu ke kokarin raba Najeriyar.

KU KARANTA: Hare haren ƙunar baƙin wake yayi ƙamari a jami’ar Maiduguri, rayuka 16 sun salwanta

“Osinbajo ya nuna jarumta ta yadda yayi wuf ya dakatar da tashin tashinan data biyo bayan kokarin raba Najeriya, da matasan inyamirai da na Arewa suka yi. Amma kokarin da Osinbajo yayi na ganawa da sarakunan gargajiyam gwamnoni, shuwagabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki ya kwantar da hankula.” Inji Atiku.

Atiku Abubakar ya jinjina ma muƙaddashin shugaban ƙasa Osinbajo

Atiku Abubakar

Daga karshe, Atiku yayi addu’ar Allah ya kara ma shugaban kasa lafiya da kuzari, sa’annan ya shawarci musulmai dasu tabbata darussan azumin watan Ramadana sun yi tasiri akansu har bayan Ramadana domin samun ingantacciyar al’ummar musulmai.

NAIJ.com ta ruwaito Atiku na kira ga Musulman Najeriya dasu yi koyi da halayya kyawawa irin na Annabi Muhammadu (S.A.W).

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya dace gwamnati ta dauki Evans aiki? kalla

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel