IBB ya caccaki masu neman wargaza Najeriya

IBB ya caccaki masu neman wargaza Najeriya

- Tsohon shugaban kasa mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya yi Allah wadai a kan masu fafutukar neman wargaza Najeriya

- IBB ya ce kalaman kiyayya da wasu tsiraru a kasar suka rika yi a wancan lokacin ya jawo yakin basasa

- IBB ya kuma nuna goyon bayansa cewa a sakewa kasar fasali ta yadda za a rabewa gwamnatin tarayya iko

Tsohon shugaban kasar mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da zaman dar dar a kasar nan yayin da ya yi Allah wadai a kan wadanda ke ci gaba da kiraye kirayen raba kasar.

A cikin wata sakon murnan bikin sallah ta Eid-el-Fitri ga ‘yan Najeriya da ya fitar, IBB ya ce Najeriya ta fuskanci yakin basasa inda aka rasa rayuka masu yawa kuma yakin ya fara ne daga irin kalaman kiyayya da wasu tsiraru suka rika yi a wancan lokacin.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, tsohon shugaban sojan ya kira gwamnati da babban murya cewa ya kamata a sakewa kasar fasali ta yadda za a rabewa gwamnatin tarayya iko.

IBB ya caccaki masu neman wargaza Najeriya

Tsohon shugaban kasa mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida

KU KARANTA: 'Duk Wanda ya zaci Najeriya zata zauna kasa daya, lallai gaula ne' - Inji Olu Falae

IBB ya kuma yi Allah wadai da kalaman kiyayya da jawabai daban-daban daga wasu kungiyoyi a kasar.

Babangida a cikin sakon sallah ya nuna goyon bayansa wajen kafa ‘yan sandan jihohi ta yanda a iya magance rashin tsaro da kuma ta’addanci a kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel