366

USD/NGN

Sultan: Rashin kyakyawar tsarin gwamnati yasa mu a cikin wannan halin – Inji Sarkin musulmi

Sultan: Rashin kyakyawar tsarin gwamnati yasa mu a cikin wannan halin – Inji Sarkin musulmi

- Sultan na Sakwato ya ce rashin kyakyawar tsarin gwamnati yasa mu a cikin halin da muke ciki yanzu

- Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya kai gaisuwan Sallah ga Sarkin Musulmi, Alhaji Saad Abubakar a fadarsa

- Wike ya ce mutanen jihar gaba daya da kuma gwamnatin jihar Rivers na goyon bayan Najeriya a matsayin kasa daya

Sarkin Musulmi Alhaji Saad Abubakar a ranar Talata, 27 ga watan Yuni ya ce rashin kyakyawar tsarin gwamnati a baya ya jawo fafutukar da wasu yankin kasar nan ke yi yanzu.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Sultan ya yi wannan magana ne a fadarsa da ke Sakwato a lokacin da ya karbi bakoncin gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, wanda ya kai masa gaisuwan Sallah.

Sultan ya ce: "A baya, wasu mutane sun aikata abubuwan da ba dai dai ba da dama ba tare da a hukunta su ba. Ire-iren wadannan yasa muka samu kan mu cikin rashin shugabanci nagari”.

Sultan: Rashin kyakyawar tsarin gwamnati yasa mu a cikin wannan halin – Inji Sarkin musulmi

Sarkin Musulmi Alhaji Saad Abubakar Rashin kyakyawar tsarin gwamnati yasa Najeriya a cikin wannan matsaloli

Sultan ya jaddada bukatar amfani da tattaunawa don warware duk rashin fahimtar juna da kuma matsaloli a kasar.

KU KARANTA: Ka ji abin da Gwamnan Ribas Wike ya fadawa mai alfarma Sarkin Musulmi

A nasa bayani gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce mutanen jihar gaba daya da kuma gwamnatin jihar Rivers na goyon bayan Najeriya a matsayin kasa daya.

Wike ya ce "Sarkin musulmi yana matsayin uban duk 'yan Nijeriya ne kuma ya kasance mai son zaman lafiya da hadin kai ‘yan Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Related news
Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe

Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe

Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe
NAIJ.com
Mailfire view pixel