Wata sabuwar doka na shirin yiwa dukkan barayin Najeriya afuwa

Wata sabuwar doka na shirin yiwa dukkan barayin Najeriya afuwa

- Ana shirin yi wa barayin gwamnatin Najeriya afuwa

- Sabuwar dakar dai na a gaban majalisar wakillai ta kasa

- An yi wa dokar karatu na farko a 14 ga watan nan na Yuni

Wata sabuwar doka da yanzu haka take a gaban majalisar wakillai ta kasa na shirin yi wa dukkan barayin kasar nan afuwa tare da yafe masu.

Ita dai wannan dokar idan ta tabbata to dukkan barayin kasar za su samu afuwar gwamnati idan har suka cika wasu muhimman sharudda da za'a gindaya masu.

Haka ma dai sabuwar dokar ba zata tilastawa barayin cewa lallai sai sun fadi inda da kuma yadda suka samu wannan haramtattun kudin na su ba.

Wata sabuwar doka na shirin yiwa dukkan barayin Najeriya afuwa

Wata sabuwar doka na shirin yiwa dukkan barayin Najeriya afuwa

NAIJ.com ta samu labarin cewa dokar dai ana so ne ta yi aiki a shekara ukku (3) kacal amma kuma ita gwamnatin ta tarayya zata iya kara wa'adin dokar idan ta ga damar yin hakan.

An dai yi wa wannan kudurin dokar karatu na daya ne a 14 ga watan nan da muke ciki a zauren majalisar wakillan yanzu haka kuma ta na jiran karatu na biyu inda za'a tafka muhawa kan ta a lokacin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel