366

USD/NGN

An tsinto gawawwakin yan gudun hijra 52 a Sahara yayinda aka ceto 600

An tsinto gawawwakin yan gudun hijra 52 a Sahara yayinda aka ceto 600

Kungiyar gudun hijran duniya wato International Organisation for Migration, IOM, ta alanta ceton akalla mutane 600 tun watan Afrilu 2017 a Sahara.

Kungiyar majalisar dinkin duniya ta kuma sanar da cewa mutane 52 yawancin yan Najeriya, Gambiya, Senegal da Cote d’Ivoire, sun hallaka a wurin, game da cewar jawabin da ta saki ranan Talata.

“Muna fadada kokarinmu wajen taimakawa yan gudun hijra a arewacin Agadez, hanyar iyakan Nijar da Libya.

“Tun daga farkon wannan shekara, munata samun kiraye-kiraye na ceton rayukan wadanda suka dau hanyar, “ Ma’aikaci Giuseppe Loprete,ya bayyana hakan.

An tsinto gawawwakin yan gudun hijra 52 a Sahara yayinda aka ceto 600

An tsinto gawawwakin yan gudun hijra 52 a Sahara yayinda aka ceto 600

Game da cewarsa, wata yar shekara 22 ce kawi ta tsira a cikin wadanda aka je ceto a ranan 28 ga watan Mayu. Ta bar Najeriya ne a watan Afrilu domin ketarawa Turai.

KU KARANTA: Kannywood: Safiya Mus tayiwa sauran yan matan fim wa'azi

“Akwai yan gudun hijra 50 akan mota yayinda suka nufi Libya daga Agadez, amma mutane 6 kawai sukr raye cikinsu,” Loprete yace.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Related news
Wata tsohuwar minista ta yi Allah wadai da kalaman mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari

Wata tsohuwar minista ta yi Allah wadai da kalaman mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari

Wata tsohuwar minista ta yi Allah wadai da kalaman mai magana da yawun shugaban kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel