Abubuwa shida da ka iya jefa mutum cikin tarkon hukumar kare haddura na kasa (FRSC)

Abubuwa shida da ka iya jefa mutum cikin tarkon hukumar kare haddura na kasa (FRSC)

-Dakokin hukumar kare haddura na kasa guda shida da ya kamata koya ya kiyaye

- Rashin bin wadannan dokokin na iya sa jami'an FRSC su kama ka

A watan fabrairu na shekara 1988, gwamnatin tarayyar Najeriya ta kirkiri hukumar kare haddura na kasa ta hayan amfani da decree mai lamba 45 na shekarar 1988 wanda aka sake ma gyaran fuska da decree ta 35 na shekara 1992 wanda a kudin tsarin mulki ake ma lakabi da FRSC Act cap 141 Laws of the federation of Nigeria (FLN).

Yan majilissan Najeriya sun zartar dashi a mastayin doka mai suna Federal Road safety Commission (FRSC) establishment Act 2007.

A kokarin cigaba da aikin su, hukumar FRSC ta ce aikata daya daga cikin wadannan abubuwan guda shida ka iya sa mutum ya shiga tarkon hukumar.

Abubuwa shida da ka iya jefa mutum cikin tarkon hukumar kare haddura na kasa (FRSC)

Abubuwa shida da ka iya jefa mutum cikin tarkon hukumar kare haddura na kasa (FRSC)

1. Amfani da wayar sallula

Yin kira ko amsa kira a waya na iya dauke hankalin mai tuki har ya kai ga hatsari.

2. Bel na mazauna kujerun gaba

Direba da pasinjan da ke zaune a gaba ya zama dole suyi amfani da bel domin kaucewa fushin hukumar. Idan hatsari ya faru pasinjan baya ma da bai daura bel ba yana iya tsale ya ji ma direba rauni ko ma yayi sanidiyar mutuwar sa.

3. Tuki bayan shan abin maye

Tuki a yayin da mutum ke cikin maye na iya gusar da hankalin mutum komin kankantar abin mayen. Saboda haka duk wanda yasha abin maye kada yayi tuki.

4. Gudu na wuce ka’ida

Wuce kimar ka’idan gudu na titi yana daga cikin manya-manyan abubuwan da ke hadasa hatsari a tituna.

5. Na’urar kashe gobara

Shin kana da na’urar kashe gobara a motar ka? Rashin wannan na’urar laifi ne da ka iya sa jami’an hukumar kare haddura na kasa su kama ka.

6. Kujerar kariya na yara

Idan kana dauke da kankanin yaro a motar ka, ka tabbatar kana amfani da mazauni na musamman da zai ba yaron kariya kuma a rika duba ingancin ta akai-akai.

A takaice dai hukumar FRSC c eke da alhakin karewa da rage haddura akan manyan tituna, saboda haka ya dace mubi dokokin da shawarwarin da suke bamu.

Har illa yau, aikin su ya hada da rage cikunso a manyan hanyoyi, shirya gangamin wayar da kai da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel