Lafiya jari ce: An samar da sabon maganin cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki

Lafiya jari ce: An samar da sabon maganin cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki

Hukumar UNITAID wadda ke da alhakin kula da saye da sayarwar ingantattun magungunan ta kasa-da-kasa tace ta kammala shire-shiren ta tsaf domin shigowa da sabon maganin cutar nan mai karya garkuwar jiki watau kanjamau musamman ma ga wadan tsaffin magungunan suka dena yi wa aiki.

Kamfunan ViiV Healthcare da ke karkashin Glazo SmithKlin ne dai suke kokarin ganin an samu maganin wanda suka sanya wa suna Dolutegravir (DTG).

Legit.ng ta samu labarin cewa gwamnatin Amurika a shekaran 2013 ta fara gwada maganin akan mutane 20,000 a kasar Kenya sannan ta amince a shigo da shi a kasashen Najeriya da Uganda.

Lafiya jari ce: An samar da sabon maganin cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki
Lafiya jari ce: An samar da sabon maganin cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki

Hukumar UNITAID ta ba da bayanai cewa mutanen da ke dauke da cutar kanjamau a kasashen da suka ci gaba za su iya zaban amfani da wannan sabuwan maganin DTG din musamman mutanen da ba su taba shan maganin cutar kanjamau ba da kuma wadanda maganin cutar kanjamau ya ki aiki a jikin su.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel