Takaitaccen tarihin tsohon Gwamnan jihar Taraba Marigayi Danbaba Suntai

Takaitaccen tarihin tsohon Gwamnan jihar Taraba Marigayi Danbaba Suntai

- An haifi Danbaba Danfulani Suntai a ranar 30 ga watan Yunin 1961 a kauyen Suntai da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba.

- Ya yi karatun sakandarensa a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kano tsakanin 1975-1980 sannan ya halarci makarantar share fagen shiga Jami'a da ke Jami'ar Ahmadu Bello University, Zaria tsakanin 1980-1981.

Ya yi karatun digirinsa a fannin hada magunguna a Jami'ar Ahmadu Bello University inda ya kammala a 1984.

Danbaba Suntai ya samu horo na sanin makamar aiki a asibitin kwararru na Yola kuma ya yi hidimar kasarsa a wani asibitin Ijaiye da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun tsakanin 1985-1986.

Legit.ng ta samu labarin cewa daga nan ne ya soma aiki a asibitin Ganye da ke tsohuwar jihar Gongola har shekarar 1991.

Suntai Suntai ya tsunduma cikin harkokin siyasa inda aka zabe shi a matsayin shugaban karamar hukumar Bali tsakanin1989-1993.

A lokacin zabukan shekarar 1999, ya zama shugaban jam'iyyar All People's Party (APP) na jihar Taraba.

Takaitaccen tarihin tsohon Gwamnan jihar Taraba Marigayi Danbaba Suntai
Takaitaccen tarihin tsohon Gwamnan jihar Taraba Marigayi Danbaba Suntai

An nada shi a matsayin kwamishinan ilimi tsakanin 2000-2003, da na lafiya tsakanin 2003-2005 kafin ya zama sakataren gwamnatin jihar Taraba tsakanin 2005-2007.

Gabanin zaben 2007, abokin Danbaba Suntai, wato Danladi Baido ya lashe zaben fitar da gwani na gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar PDP amma daga bisani an haramta masa takara.

Wata biyu bayan haka ne, PDP ta maye gurbinsa da Danbaba Suntai, wanda bai tsaya zaben fitar da gwanin ba.

Baido ya goyi bayan Suntai, kuma a watan Afrilun 2007 aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Taraba.

An zabe shi a karo na biyu ranar 26 ga watan Afrilun 2011.

Tsohon gwamnan jihar ta Taraba ya yi hatsari a jirgin da yake tukawa ne a watan Oktoban 2012, inda ya samu matsala a kwakwalwarsa.

Suntai ya rasu ranar 28 ga watan Yunin 2017 yana da shekara 56.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel