Dalilin da ya sa ba a gurfanar da Evans a gaban Kotu ba -Jami'an 'Yan Sanda

Dalilin da ya sa ba a gurfanar da Evans a gaban Kotu ba -Jami'an 'Yan Sanda

- Evans yace an shiga hakkin shi kan tsare shi da aka yi

- Evans mai sana'ar garkuwa da mutane ya kai karar Jam'ian 'Yan Sanda Kotu

- Jami'an 'yan Sanda na kokarin binciko sauran da suke mu'amala

Hukumar ‘Yan Sanda sun bayyana dalilin da ya sa ba a gurfanar da mai garkuwa da mutane Chukwudumeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans ba a gaban Kotu.

A ranar laraba ne Evans ya kai karar Insfakta Janar na 'Yan Sanda Ibrahim Idris da Kwamishina na 'Yan Sanda na Jahar Legas a babbar Kotu da ke Jahar Legas.

KU KARANTA KUMA: Bautar da ‘ya’yan mutane da sunan karatun Al-Qur’ani (hotuna)

Dalilin da ya sa ba a gurfanar da Evans a gaban Kotu ba -Jami'an 'Yan Sanda

Dalilin da ya sa ba a gurfanar da Evans a gaban Kotu ba -Jami'an 'Yan Sanda

Evans ya bayyana dalilin shi a kan cewa 'ci gaba da tsare shi a wurin Jami'an 'Yan Sanda shiga hakkin Dan Adam ne '

Hukumar yan sanda tana tsare da Evans da sauran mutranen da yake mu’amala da su a kan harkar garkuwa da mutane , zata tsare su har na tsawon watanni uku

Yin hakan ne zai ba jamian yan sanda damar yin kwakwwaran bincike har a gano sauran da suke da hannu a cikin sana’a ta garkuwa da mutane da Evans yake shugaban su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Donald Trump ya ki taimakawa Musulman Rohingya da su kayi gudun hijira

Donald Trump ya ki taimakawa Musulman Rohingya da su kayi gudun hijira

Donald Trump ya ki taimakawa Musulman Rohingya da su kayi gudun hijira
NAIJ.com
Mailfire view pixel