Labarin wasanni: Jamus ta isa wasan karshe bayan ta doke Meziko

Labarin wasanni: Jamus ta isa wasan karshe bayan ta doke Meziko

– Meziko tayi waje daga Gasar zakarun Nahiyoyi jiya

– Jamus za ta fafata da Kasar Cili a wasan karshe

– Kasar Meziko ta sha mugun kashi a hannun Jamus

Meziko ta sha dan karen kashi a wasan ta da Kasar Jamus. Yanzu dai an yi waje da Focugal da kasar ta Meziko. Kasar Cili ce za ta kara da Zakarun Duniya Jamus.

Labarin wasanni: Jamus ta isa wasan karshe bayan ta doke Meziko

Dan wasa Goretzka na Jamus ya jefa kwallaye 2

Dama jiya ku ka ji cewa Chile za ta kara da Kasar Meziko ko Jamus a wasan karshe. Yanzu haka Zakarun Duniya watau Jamus ne su isa wasan karshen bayan ta doke Meziko da ci 4-1 a jiya da dare.

KU KARANTA: Real Madrid tayi magana game da Ronaldo

Labarin wasanni: Jamus ta isa wasan karshe bayan ta doke Meziko

Jamus ta isa wasan karshe jiya da dare

Duk da Kasar Jamus yara ta zuba a Gasar na Nahiyoyi Duniya ta isa wasan karshe. ‘Yan wasa Wener da Amin Jaones ne su ka zurawa Jamus din kwallaye inda Dan wasa Goretzka ya jefa kwallaye 2 shi kadai. Yanzu haka za ta fafata da Kasar Chile ta su Sanchez da Vidal.

Shekaran jiya ne dai a gasar na zakarun Nahiyar Duniya Cili tayi waje da Kasar Focugal. Gola Carlos Bravo mai tsaron gida ya nuna bajinta bayan ya kabe dukkanin bugun na daga kai-sai mai tsaron gida.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gida kan dutse ya kama da wuta a Abuja

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel