Abinciccika 6 da ke tsufar da mutum tun kafin lokacin tsufan sa

Abinciccika 6 da ke tsufar da mutum tun kafin lokacin tsufan sa

A wani bincike da majiyar mu ta gudanar wanda aka samadashi a shafunan kiwon lafiya ta duniya ya nuna cewa lallai akwai wasu nau’ukan abinci da mutum zai ci kuma su sashi ya nuna tsufa da wuri.

Legit.ng a kokarin ta na ganin kiyon lafiya ya yawaita a al'ummar mu sun samu cewa ga wasu nan:

1. Yawan shan gishiri a abinci na da matukar illa a jikin dan yana dauke da sinadarin da ake kira Sodium wanda ke iya hana jikin mutum fitar da ruwan da jiki baya bukata wanda hakan kuma ke kawo kiba a jikin sa sosai.

2. Shan lemun zaki na kwalba da na gwangwani wanda yake dauke da sinadari a cikinsa da ake kira Acidity wanda ke canza launin hakoran dan adam.

Abinciccika 6 da ke tsufar da mutum tun kafin lokacin tsufan sa
Abinciccika 6 da ke tsufar da mutum tun kafin lokacin tsufan sa

3. Shan yaji na babu gaira babu dalili domin yana kawo tsufan fatar jikin mutum musamman matan da suka daina haihuwa.

4. Konannen burodi, Cake da sauran su domin suna sa mutum ya tsufa da sauri. Abun da ya kamata shine kafin a ci idan dai ya zama dole sai a kankare inda ya kone ko kuma a hakura da ci abincin kawai.

5. Shan shayi mai madara musamman bakin shayi wanda ake kira da Black Tea a turance domin rage bata hakoran da yake yi da kuma tsufan da ya kan sa mutum yayi.

6. Shan giya domin tana kawo kiba a jiki, sannan kuma tana hana mutum samun isashshen barci wanda hakan ke canza fatar jiki.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel