An yi jana’izar wani dan’uwar shugaba Buhari a Daura

An yi jana’izar wani dan’uwar shugaba Buhari a Daura

- An yi jana’izar wani dan’uwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura

- Marigayin na matsayin wa ga Mamman Daura babban aminin shugaban kasa

- Shugaba Buhari ya kasance kawun Mamman Daura koda ya ke Daura ya girmi shugaba Buhari da shekaru 3

An yi jana’izar wani dan’uwar shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma wa ga Mamman Daura a ranar juma’a, 30 ga watan Yuni a garin Daura da ke jihar Katsina.

A cewar jaridar Sahara Reporters, an yi jana’izar marigayin ne bisa addinin Musulunci a Daura garin shugaban kasa.

Kamar yadda aka sani, Daura na matsayin da ne ga wani wan shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma ya girmi shugaban da shekaru 3.

An yi jana’izar wani dan’uwar shugaba Buhari a Daura

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

KU KARANTA: APC ta ba da bayani a kan lafiyar Buhari, ta yi tsokaci a kan lokacin dawowar shugaban kasar

Ko da yake shugaba Buhari na matsayin kawunsa ne, amma mutanen biyu suna shiri da juna sosai.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar Mamman Daura dan jarida ne kuma ya yi aiki a matsayin shugaban na Afirka International Bank da kuma shugaban kwamitin na gidan talabijan na gwamnatin tarayya wato Nigerian Television Authority (NTA).

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
An sace wasu Turawa a Najeriya bayan sun zo raba magani

An sace wasu Turawa a Najeriya bayan sun zo raba magani

Babbar magana: An sace wasu Turawa 4 a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel