YANZU YANZU: Gawar Maitama Sule ya iso Abuja

YANZU YANZU: Gawar Maitama Sule ya iso Abuja

- Gawar Danmasanin Kano, Maitama Sule ya iso babban birnin tarayya Abuja

- Shugaban ma’aikata na tarayya, Abba Kyari, ne ya karbi gawar

- Za’a dauki gawar zuwa jihar Kano, a cikin wani jirgin fadar shugaban kasa

Gawar Danmasanin Kano, Maitama Sule da ya rasu a ranar Litinin, 3 ga watan Yuli a kasar Masar, ya iso babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban ma’aikata na tarayya, Abba Kyari, ne ya karbi gawar a ranar Talata, 4 ga watan Yuli tare da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jana’izar Danmasanin Kano.

Jirgin dake dauke da gawar ya iso da misalin karfe 1:54 na rana.

Za’a dauki gawar zuwa jihar Kano, a cikin wani jirgin fadar shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Za’ayi jana’izar Danmasanin Kano a yau Talata da Misalin Karfe huduZa’ayi jana’izar Danmasanin Kano a yau Talata da Misalin Karfe hudu

Wasu daga cikin masu fada aji dake Kano suna jiran isowar gawar sun hada da Ango Abdullahi, gwamnan jihar Jigawa, gwamnan jihar Bauchi da kuma tawaga daga jumhuriyyar Nijar.

Idan zaku tuna NAIJ.com ta rahoto cewa a ranar Litinin, gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa za’ayi jana’izar sa da misalin karfe 4 na ranar Talata a fadar sarkin Kano.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Zaben 2019: Jam'iyyar APC tayi asarar mutane 20,000 zuwa PDP a jihar Kano

Zaben 2019: Jam'iyyar APC tayi asarar mutane 20,000 zuwa PDP a jihar Kano

Zaben 2019: Jam'iyyar APC tayi asarar mutane 20,000 zuwa PDP a jihar Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel