366

USD/NGN

Siyasa: Wani jigon jam’iyyar APC ya sallake rijiya da baya

Siyasa: Wani jigon jam’iyyar APC ya sallake rijiya da baya

- Allah ya ceci wani jogon jam’iyyar APC a hannun ‘yan kisan gilla a jihar Bayelsa

- Ikiogha ya koka ga ‘yan sanda kafin wannan hari cewa wasu mutane na barazana da rayuwarsa

- 'Yan kisan gilla su 5 suka cusa a gidan da siyasan a dai dai karfe 2am na safiya

Wani jigon jama'iyyar mai mulki APC a shiyar Jihar Bayelsa, Cif Dikivie Ikiogha, ya sallake rijiya da baya a lokacin da wasu ‘yan kisan gilla suka kai masa hari a gidansa da ke yankin Kpansia a garin Yenagoa, babban birnin jihar a ranar Lahadi, 3 ga watan Yuli.

Kammar yadda NAIJ.com ta samu labari cewa wasu 'yan kisan gilla 5 wadanda ke tare da bindiga mai kerar AK47 sun cusa gidan Ikiogha wanda ke da iyaka da gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a garin Yenagoa a dai dai karfe 2 am na safiya.

Amma Ikiogha, wani aminin tsohon shugaban kasa Jonathan kuma tsohon shugaban ma’aikatan fadan gwamnati jihar na gwamna Seriake Dickson, rahotanni sun tabbatar cewa ba ya gidan a lokacin da 'yan bindiga suka kai hari a gidan.

Siyasa: Wani jigon jam’iyyar APC ya sallake rijiya da baya

'Yan kisan gilla masu rike da AK47 Source: today.ng

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya sun gano gurin kera makamai a Delta, an kama mutane 18

Majiyar ta ce kafin wannan harin, Ikiogha ya koka ga ‘yan sandan jihar cewa wasu mutane na barazana da rayuwarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Related news
Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe

Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe

Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe
NAIJ.com
Mailfire view pixel