Yaƙi da rashawa: Shuwagabannin ƙasashen nahiyar Afirka sun baiwa Buhari wani gagarumin aiki

Yaƙi da rashawa: Shuwagabannin ƙasashen nahiyar Afirka sun baiwa Buhari wani gagarumin aiki

Kafatanin shuwagabannin kasashen nahiyar Afirka sun amince da nada shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin jagoran yaki da cin hanci da rashawa a nahiyar gaba daya.

Wannan sabon nadi ga shugaba Buhari ya biyo bayan taron shuwagabannin nahiyar ne daya gudana a babban ofishin kungiyar kasashen Afirka dake Adis Ababa, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

KU KARANTA: Buhari zai iya mulkin Najeriya ko a keken Guragu yake – Tsohon Soja

Ana sa ran Buhari zai jagoranci wani taro na musamman akan hanyoyin yaki da rashawa a shekarar 2018, wanda aka yi ma taken “Samun nasarar yaki da rashawa: Hanyar ciyar da Afirka gaba.”

Yaƙi da rashawa: Shuwagabannin ƙasashen nahiyar Afirka sun baiwa Buhari wani gagarumin aiki

Taron Shuwagabannin ƙasashen nahiyar Afirka

A jawabin Ministan harkokin kasashen waje na Najeriya, Geofrey Onyeama yace wannan nadi da aka yi ma Buhari sakamako ne na kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen yaki da rashawa tare da tarin nasarorin da take samu.

“Ina ganin abin dubawa a nan, shine shugaba Buhari ya zama kamar tauraro abin kallo musamman wajen yaki da rashawa, tare da kawo cigaba mai daurewa a nahiyar Afirka.” Kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito ministan na fadi.

Da wannan mukami, ana sa ran shugaba Buhari zai yi aiki kafada da kafada da sauran shuwagabannin kasashen Afirka tare da yi musu jagora wajen sanar dasu sirrin yaki da rashawa da koyar dasu hanyoyi yaki da rashawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ina Buhari ya shiga ne?

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel