Zan daina yin rawa da waka a Fim, amma….. – Inji Ali Nuhu (KARANTA)

Zan daina yin rawa da waka a Fim, amma….. – Inji Ali Nuhu (KARANTA)

- Jarumin Kannywood Ali Nuhu yace zai daina rawa da waka

- Sai dai shahararren dan wasan Hausan bai bayyana yaushe ne ba

Shahararren dan wasan Kwaikwayo na Kannywood Ali Nuhu wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood ya bayyana ma BBC Hausa cewa ya kusa daina rawa da waka, amma fa sai idan lokaci yayi.

Sarki Ali yace sau dayawa ya kan yi rawa da waka ne kadai idan hakan ya zama dole, musamman idan Fim din na bukatar ayi hakan.

KU KARANTA: Kwaya ce: Ýan mata da matan Aure sun koma harkar shan ƙwaya da kayan maye – Inji NDLEA

Sarki Ali ya kara shaida ma majiyar Legit.ng cewar idan da za’a kwatan ta irin rawar da yake yi a baya, za’a gane cewa ya rage sosai.

Zan daina yin rawa da waka a Fim, amma….. – Inji Ali Nuhu (KARANTA)
Ali Nuhu

Sai dai jarumin Fim din Hausan, wanda a yanzu shekarunsa 44 bai bayyana yaushe ne ranar da zai daina yin rawa ba. A wani hannun kuma a kwanan nan ne Ali Nuhu ya fitar da sabon Fim dinsa Mansoor, wanda masana suke ganin ya kawo sabon salo a Kannywood.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani Minista kake son ganin Buhari ya sallama?

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel