Abinci 5 da ke sa warin kashi da jiki

Abinci 5 da ke sa warin kashi da jiki

Wani kwararren likita a asibitin kwararru dake jihar Kaduna, Ankama ya ba mutane shawarwari bisa irin nau’in abinci da ke haddasa warin kashi idan yawan ta'ammali da su.

Ya bayyana nau'i-nau'i na abincin kamar haka:

1. Yawaita yin ta'ammali da yaji, albasa da tafarnuwa ka iya haifar da matsalar warin kashi saboda suna tattare da wata sindari mai suna ‘Sulfur’ wanda ke fita ta ramukan da gumi ke fita a jikin mutum wanda hakan ke haddasa warin jiki da kashi.

2. Kayan marmari da akeyi da filawa; likitan ya ce kayan makulashe irin su cakulet, gyada, biskit, da sauran abubuwa dake kara kiba a jiki wanda hakan kan iya kawo wannan matsala da ake magana a kanta. Likitan ya shawarci yawan cin wannan abubuwa da su yawaita motsa jiki.

Abinci 5 da ke sa warin kashi da jiki
Kayan makulashe

3. Cin abincin da basa tattare da sinadarin ‘Carbonhydrates’ na kawo gumi wanda idan ba ana yi ana gyara jiki bane sai ka ga ana dan bashi-bashi.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTA

4. Yawan cin kifi.

Abinci 5 da ke sa warin kashi da jiki
Yawaita cin kifi

5. Yawaita cin nama na haifar da wannan cuta da ake magana a kanta domin idan ya taru a jikin mutun ya kan hadu da ‘Bacteria wanda ke sa warin kashi.

Abinci 5 da ke sa warin kashi da jiki
Yawan cin naman sa

Ankama ya kara da cewa idan har mutane na so su kare kansa daga wannan cuta to sai ya yawaita cin wasu ganyayyaki da ake ci kamar irin su Lansuru da kayan marmari na itatuwa irin su lemun zaki, lemun tsami, tufa da dai sauran su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel