EFCC: Gwamnoni sun tasa Ibrahim Magu a gaba

EFCC: Gwamnoni sun tasa Ibrahim Magu a gaba

- Shugaban Gwamnonin Najeriya Abdulazeez Yari ya soki Magu

- Yace za su sa kafar wando daya da Shugaban Hukumar EFCC

- EFCC na bincike kan wasu kudi da aka ba wasu Gwamnoni Najeriya

Gwana Abdulazeez Yari na Jihar Zamfara yayi kaca-kaca da Hukumar EFCC. Hukumar na bincike kan wasu kudi da aka ba wasu Gwamnoni Najeriya wanda kusan haka ke nema ya jawo rikici.

EFCC: Gwamnoni sun tasa Ibrahim Magu a gaba

Hoton Ibrahim Magu na EFCC da daya daga cikin Gwamnoni

Gwamna Yari yace sam Hukumar ba ta san aikin da ta ke yi ba. Yari yace ba Gwamnoni kadai ya kamata a zarga ba wajen aikata laifi don haka dole a shafa masu lafiya. Gwamnan yace idan EFCC za tayis ai a shirya.

KU KARANTA: Jakadan Najeriya ya yabawa 'Yan kasar

EFCC: Gwamnoni sun tasa Ibrahim Magu a gaba

Hoton Shugaban Gwamnonin Najeriya Yari

Gwamnan dai yace zai rubutawa Gwamnatin Buhari wasika domin ta san cewa rashin kunyar yayi yawa don Ibrahim Magu bai isa ya taba su ba a matsayin sa na Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda.

Jiya Mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin rashawa Farfesa Itse Sagay yace game da batun Magu na EFCC kuma an gama magana tun bayan da Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yace ba za a tsige sa ba kuma ta zauna.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za ka iya barin Najeriya [Bidiyo]

Source: Hausa.naij.com

Related news
Magoya bayan Ali Modu Sheriff na ci gaba da ficewa zaga PDP

Magoya bayan Ali Modu Sheriff na ci gaba da ficewa zaga PDP

Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP magoya bayan Ali Modu Sheriff sun shilla zuwa APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel