An matsa mun lamba da na yi murabus a matsayin shugaban majalisar dattawa – Inji Saraki

An matsa mun lamba da na yi murabus a matsayin shugaban majalisar dattawa – Inji Saraki

- Shugaban Majalisar Dattawa ya ce wasu mutane sun matsa lamba da ya yi murabus a matsayin shugaban majalisar

- Saraki yace ya ki yin murabus ne saboda wahalar da kuma gudumawarsa ga nasarar jam’iyyar APC

- Saraki ya nuna godiyarsa ga sarkin Ilorin cewa ya kasance tare da shi daga farko har karshen shari’ar

Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Bukola Saraki, a ranar Juma'a, 7 ga watan Yuli ya bayyana cewa ya kasance karkashin tsanani matsa lamba da ya yi murabus a lokacin da yake fuskantar sharia’a a kotun da’a (CCT).

Saraki, da yake magana da magoya bayansa a Ile Arugbo sashe na garin Ilorin babban birnin jihar Kwara, ya ce ya ki yin murabus ne saboda gudummawarsa ga nasarar jama'iyyar mai mulki ta APC a zaben shekarar 2015.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, shugaban majalisar ya dangana sakamakon nasararsa a CCT ga Allah da kuma goyan bayan mabiyansa.

An matsa mun lamba da na yi murabus a matsayin shugaban majalisar dattawa – Inji Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Bukola Saraki Source: dailypost.ng

Ya ce: “ Mun gode Allah ga ranar yau domin a lokacin da aka fara wannan rikicin a nan wurin muka hadu kuma muka yi imani cewa wata rana zamu sake hadu don nuna godiya ga Allah a kan batun kuma gashi yanzu haka din ta tabbata”.

KU KARANTA: Shugaban majalisar tarayya Bukola Saraki zaiyi tankade da rauraya na kwamitocin majalisa

“Kuma ina so in gode ma mai martaba sarkin Ilorin a kan goyon bayan da ya bamu daga farko har karshen wannan shari’a. Gudumawar nasa ya kai har wani lokaci ya ce ba zai sake rokan kowa a kan lamarin ba, ya ce yanzu zamu koma yin addua’a saboda babu laifin da muka yi kuma da yarda Allah zamu yi nasara” .

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Shugaba Muhammadu ya halarci zama da Donald Trump

Shugaba Muhammadu ya halarci zama da Donald Trump

Shugaba Muhammadu ya halarci zama da Donald Trump
NAIJ.com
Mailfire view pixel