Da dukiyar Arewa aka hako fetur din Najeriya-Marigayi Danmasanin Kano

Da dukiyar Arewa aka hako fetur din Najeriya-Marigayi Danmasanin Kano

- A wata hira da aka yi kafin Dan Masanin Kano ya rasu yayi dogon bayani kan Najeriya

- Marigayi Maitama ya bayyana yadda Arewa ta taka rawar gani wajen nemo fetur

- Tsohon Ministan yace an yi amfani da dukiyar Arewa wajen hako man

Tsohon Ministan mai kuma kusan na farko bayan an samu 'yanci wanda kuma shi ne wanda ya fi dadewa a kujerar yace an yi amfani da dukiyar Arewa wajen hako man fetur a Kudu.

Da dukiyar Arewa aka hako fetur din Najeriya-Marigayi Danmasanin Kano
Marigayi Danmasanin Kano Maitama Sule

Marigayi Maitama Sule yace ba zai manta ba lokacin da Kamfanin Shell su ka zo Najeriya neman man fetur a Kudancin Najeriya. Arewa ta bada wasu kudi da ta adana a matsayin na ta kason domin a samu fetur.

KU KARANTA: Yadda Abacha yaa kusa kashe ni - Obasanjo

Da dukiyar Arewa aka hako fetur din Najeriya-Marigayi Danmasanin Kano
Masu fasa kaurin hako fetur a Najeriya

Tsohon Ministan yace ba a ga dalilin wata yarjejeniya ba don kuwa Ministan tsaro na wancan lokacin Muhammad Ribadu yace duk kasa daya ake ciki. Marigayin ya rike Ministan mai amma ko kudin mota aro ya nema bayan an kifar da Gwamnati ba ma rijiyar mai ba.

Kasashen da su ka dogara da man fetur sai su sake tunani don kuwa irin su kasar Faransa kamar yadda mu ka samu labari su na shirin daina amfani da duk wani abin hawa da ke aiki da man fetur ko dizil nan da shekarar 2040 kamar yadda wani Ministan kasar ya bayyana.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hira da Jama'a domin ji ko za su iya barin Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel