Dangote baya tattalin dukiya - Seun Kuti

Dangote baya tattalin dukiya - Seun Kuti

- Ance dai iya ruwa fidda kai

- Dan Fela Kuti ya kalubalanchi Dangote

- Seun Kuti ya bayyan ra’ayin shi

Dan shaharerren tsohon mawakin Najeriya Fela Kuti, ya kalubalanci Alhaji Aliko Dangote da wulakantar da dukiya saboda ganin yadda yake wadaka da dukiyar da Allah ya bashi.

Seun Kuti dan kimamin shekaru 34 a duniya, ya bayyan cewa Dangote baya duba da talakawan kasar nan saboda ganin irin yadda yake kashe dukiyar sa akan gaira babu dalili.

Dangote baya tattalin dukiya - Seun Kuti

Dangote baya tattalin dukiya - Seun Kuti

Mawakin Seun Kuti, wanda shima ya gaji harkar yin waka ne a wajen mahaifinshi, ya watsa hotunan Dangote da abokanshi a cikin wanin jirgin ruwa na alfarma duba da irin yadda suke fantamawa.

KU KARANTA: Madalla! Kamfanoni sumunti zasu rage farashin sumuntin su a Najeriya

Seun ya nuna damuwarsa kwarai, ya ce banda basussuka na kudi da ake bin shi Dangote da abokan na sa na kimanin kudi Naira tiriliyan 2.5 amma suke irin wannan sharholiya da nuna halin ko oho akan talakawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
'Yan Arewa Da Buhari Suka Yarda, Basu Yarda Da Atiku ba - Farfesa Akinyemi

'Yan Arewa Da Buhari Suka Yarda, Basu Yarda Da Atiku ba - Farfesa Akinyemi

'Yan Arewa Da Buhari Suka Yarda, Basu Yarda Da Atiku ba - Farfesa Akinyemi
NAIJ.com
Mailfire view pixel