Ambaliya a Suleja ya kashe mutum 20 (hotuna)

Ambaliya a Suleja ya kashe mutum 20 (hotuna)

- Akalla mutane ashirin ne suka mutu a yankin Suleja dake jihar Niger

- Hakan ya afku ne sanadiyar ambaliyar ruwa sakamakon ruwa mai karfi da tafka a yankin

Kimanin mutane 20 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon wata ambaliya day a afku bayan wani rowan sama da akayi kamar dab akin kwarya a kananan hukumomi dake Suleja da Tafa dake jihar Niger.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutane 11 sun mutu a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli. Daga cikin mutane sha dayan da suka mutu, 9 sun mutu ne a yankin Checheniya, daya a Kuspa, yayin da dayan kuma a ya rasu a Hayin Nassarawa dukkansu a karamar hukumar Tafa.

KU KARANTA KUMA: An cigaba: An kirkiro wayar da ba ta aiki da batiri

A ranar Litinin, 10 ga watan Yuli yawan mamatan ya tashi zuwa 20 bayan hukumar dake bayar da agajin gaggawa ta jihar ta samo sababbin gawawwaki guda takwas.

Har yanzu dai ana ci gaba da duba guraren ambaliyar rowan ta afku domin gano Karin gawawwaki.

Kalli hotunan ambaliyar a kasa:

Ambaliya a Suleja ya kashe mutum 20 (hotuna)
Guraren da ambaliyar ya afku Hoto: Alummata

Ambaliya a Suleja ya kashe mutum 20 (hotuna)
Ruwan ya yi barna sosai Hoto: Alummata

Ambaliya a Suleja ya kashe mutum 20 (hotuna)
Ambaliya a Suleja ya kashe mutum 20 Hoto: Alummata

Ambaliya a Suleja ya kashe mutum 20 (hotuna)
An gano gawawwakin mutane 20 Hoto: Alummata
Asali: Depositphotos

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel