Toh fa: Wani gwamnan APC ya dakatar da sarakunan gargajiya daga magana da harshen Turanci

Toh fa: Wani gwamnan APC ya dakatar da sarakunan gargajiya daga magana da harshen Turanci

- Gwamnan jihar Imo ya gargadi sarakunan gargajiya da su kaurace yin amfanin da harshen Turanci

- Okorocha ya ce dole ne sarakunan su gudanar da ayyukansu a harshen Igbo

- Okorocha ya mika sandar sarauta da takardar shaida ga sarakunan gargajiya 19 a jihar

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo, ya dakatar da sarakunan gargajiya a jihar daga yin magana da harshe Turanci a bainar jama'a ko kuma lokacin gudanar da taro a garuruwansu.

Okorocha ya ba da wannan umarni ne a yau Talata, 11 ga watan Yuli a lokacin da yake bikin mika sandar sarauta da takardar shaida ga wasu sarakunan gargajiya 19 a fadar gwamnati da ke Owerri.

Gwamnan ya ce dole ne sarakunan gargajiya a jihar su gudanar da ayyukansu a harshen Igbo, ko kuma su samu mai fassara masu.

Toh fa: Wani gwamnan APC dakatar da sarakunan gargajiya daga magana da harshen Turanci

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo

KU KARANTA: Wani Sarkin Yarbawa yayi kira a sauya tsarin Kasar nan

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar gwamna Okorocha ya kasance daya daga gwamnonin yankin kudu maso gabashin kasar kuma dan jam'iyyar APC mai mulki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Zaben 2019: Jam'iyyar APC tayi asarar mutane 20,000 zuwa PDP a jihar Kano

Zaben 2019: Jam'iyyar APC tayi asarar mutane 20,000 zuwa PDP a jihar Kano

Zaben 2019: Jam'iyyar APC tayi asarar mutane 20,000 zuwa PDP a jihar Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel