LABARI DA DUMI-DUMI: Kamfanin sadarwa na Etisalat ta canza sunan ta zuwa 9Mobil

LABARI DA DUMI-DUMI: Kamfanin sadarwa na Etisalat ta canza sunan ta zuwa 9Mobil

- Kamfanin sadarwa na Etisalat ta Najeriya ta canza sunan ta zuwa 9Mobile Telecom

- Kamfanin sadarwa na Etisalat na kasa da kasa ta bukaci Etisalat Najeriya ta canza sunan nan da makonin uku

- Shugabannin kamfanin sadarwa ta Etisalat ta bayyana sabon sunan bayan taron ta a Legas

Shugabannin kamfanin sadarwa ta Etisalat bayan karshen wani taron ta a Legas ta canza wa kamfanin sabon suna daga Etisalat zuwa 9Mobile.

Legit.ng ta ruwaito cewa uwar kamfanin Etisalat wato Emirates Telecommunications Corporation(ETC) ta bukaci Etisalat ta Najeriya ta dakatar da yin amfani da sunan kamfanin nan da makonni uku.

A farkon makon nan ne babban shugaban kamfanin, Hatem Dowidar ya sanar da cewa kamfanin za ta rufe kasuwancinta a Najeriya daga kamfanonin sadarwar kasar nan da makonni Uku masu zuwa.

LABARI DA DUMI-DUMI: Kamfanin sadarwa na Etisalat ta canza sunan ta zuwa 9Mobil
Ofishin kamfanin sadarwa na Etisalat

KU KARANTA: Ziyarar Osinbajo ga Buhari yaudara ne – Fayose

Kamfanin Etisalat Najeriya ta ciwo bashin dala Amurka biliyan 1.2 daga bankunan kasar 13 wanda tun a shekarar 2013 wanda suka kasa biya har yanzu bayan shekaru hudu da ciwo bashin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel