• 363

    USD/NGN

Ta’addanci: Wasu ‘yan bindiga sun halaka wani soja a Delta

Ta’addanci: Wasu ‘yan bindiga sun halaka wani soja a Delta

- Wasu 'yan bindiga a yankin Neja Delta sun halaka wani soja inda suka jikkata wasu

- ‘Yan bindigar sun yi awon gaba da wasu manyan-manyan makamai

- ‘Yan bindigar sun raunata wani jami’in Sibil Difens a harin

Wasu 'yan bindiga a misali karfe 2 na dare a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli sun mamaye dakaru da ke Ogbogbagbene a yankin karamar hukumar Burutu a Jihar Delta, inda suka kashe wani soja, yayin da suka jikkata wasu jami’an, suka kuma yi awon gaba da wasu manyan-manyan bindigogi.

‘Yan bindigar da ba san ko su wanene ba, sun raunata wani jami’in Sibil Difens a harin. Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun rinjaye sojojin da ke bakin aiki a wannan lokacin.

Kauyen Ogbogbagbene ne garinsu tsohon ministan Neja Delta a gwamnatin da ta gabata na tsohon shugaban kasar Gooduck Jonathan, Dattijon Godsday Orubebe.

Ta’addanci: Wasu ‘yan bindiga sun halaka wani soja a Delta

‘Yan bindigar da ba san ko su wanene ba

Kwamishinan 'yan sanda, na jihar Delta, Mista Zanna Ibrahim, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Majiyar NAIJ.com, ya ce: “ Wasu ‘yan bindigar da ba san ko su wanene ba sun kai hari wani kauye a karamar Hukumar Burutu, inda suka kashe wani soja da kuma jikkata wasu”.

KU KARANTA: Boko Haram sun kuma kai hari a iyakar Kamaru da Najeriya, mutane 16 sun mutu

Ibrahim ya bayyana cewa, 'yan sanda karkashin jagoranci wani babban jami'in' yan sanda, DPO na Burutu sun sa idanu a halin da ake ciki yanzu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Related news

Gwamnatin jihar Borno na shirin dauka ma'aikata masu digiri 300 aiki

Gwamnatin jihar Borno na shirin dauka ma'aikata masu digiri 300 aiki

Gwamnatin jihar Borno na shirin dauka ma'aikata masu digiri 300 aiki
NAIJ.com
Mailfire view pixel