Wani Sanatan Arewa ya kare Shugaban kasa Buhari daga zargi

Wani Sanatan Arewa ya kare Shugaban kasa Buhari daga zargi

- Sanata Shehu Sani na Jihar Kaduna ya gargadi su Janar TY Danjuma

- Wasu Kiristocin Yankin sun ce Gwamnatin Buhari na da makarkashiya

- Sanatan yace babu wani yunkuri na tursasawa Jama’ar kasar Musulunci

Sanata Shehu Sani ya gargadi manyan Kiristocin Arewa irin su Janar TY Danjuma da ke kukan cewa Gwamnatin Buhari na da makarkashiya na tursasawa ‘Yan kasar addini Musulunci.

Wani Sanatan Arewa ya kare Shugaban kasa Buhari daga zargi

Shugaban kasa Buhari na da makarkashiya-Danjuma

Sanatan na tsakiyar Jihar Kaduna ya dauki lokacin sa a shafin sa na Facebook inda yace Gwamnatin Buhari ba ta da wannan aniya wanda idan da har akwai da shi zai fara magana. Shehu Sani ya kira Dattawan kasar su nemi yada zaman lafiya.

KU KARANTA: Sule Lamido yayi magana game da rikicin PDP

Wani Sanatan Arewa ya kare Shugaban kasa Buhari daga zargi

Hoton Sanata Shehu Sani daga Jaridar Daily Post

Manyan Kiristocin Arewa sun zargi wannan Gwamnati da manufar tursasawa Jama’ar kasar Musulunci da karfi da yaji wanda Shehu Sani yace irin wannan kalamai na iya tada kasar tsaye idan ba ayi wasa ba.

Yau kun ji cewa Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya kara jaddada cewa shi zai karbi mulki daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Farfesa Yemi Osinbajo a zaben 2019.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan Najeriya sun yi magana game da Ministocin Buhari

Source: Hausa.naij.com

Related news
Kamata yayi Buhari ya maida albashi mafi karanci N145,000 - Sanata Shehu Sani

Kamata yayi Buhari ya maida albashi mafi karanci N145,000 - Sanata Shehu Sani

Kamata yayi Buhari ya maida albashi mafi karanci N145,000 - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel