An fara kutungwilar nada El-rufai magajin Buhari a 2019

An fara kutungwilar nada El-rufai magajin Buhari a 2019

Labarin da yake ta yaduwa a bakunan mutane musamman ma a Kudancin Najeriya shine wai makusantan shugaba Buhari sun soma kishin-kishin din nada El-rufai magajin Buhari a zabe mai zuwa na 2019.

Babban dan adawar shugaba Buhari kuma jigo a jam'iyya mai mulki ta APC Femi Fani Kayode ne ya kwammata hakan a shafin sa na sada zumunta na Tuwita a ranar jiya Juma'a 14 ga watan Yuli.

An fara kutungwilar nada El-rufai magajin Buhari a 2019

An fara kutungwilar nada El-rufai magajin Buhari a 2019

NAIJ.com ta samu labarin cewa Fani-Kayode yace za’a nada gwamnan jihar Kadunan a matsayin mataimakin shugaban kasa kafin 2019 sannan kuma zai zamo shugaban kasa a 2019 din a cikin shirin su.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a makon da ya gabata ne dai kotun koli ta kasa ta tabbatar da bangaren Makarfi wanda mafi yawan magoya bayan jam'iyyar PDP suke so ciki hadda Femi Fani Kayode din a matsayin halastaccen shugabanta.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Shugaba Muhammadu ya halarci zama da Donald Trump

Shugaba Muhammadu ya halarci zama da Donald Trump

Shugaba Muhammadu ya halarci zama da Donald Trump
NAIJ.com
Mailfire view pixel