Bututun iskar gas ta fashe a gidan mai, mutane 9 sun halaka

Bututun iskar gas ta fashe a gidan mai, mutane 9 sun halaka

- Bututun iskar gas ta fashe a gidan mai, ta hallaka mutane 9

- An samu mutane da dama da suka jikkata sakamakon fashewar bututun gas

Wasu rahotanni daga majiya mai karfi sun tabbatar da mutuwar mutane 9 sakamakon wata gobara data faru sanadiyyar fashewar bututun iskar gas a wata gidan mai dake jihar Kross Ribas.

BBC Hausa ta ruwaito akalla kimanin mutane 10 ne suka samu raunuka daban daban a sanadiyyar afkuwar lamarin, sai dai majiyar NAIJ.com ta ruwaito ba’a gano menene dalilin fashewar bututun ba.

KU KARANTA: Masu min kallon jahili zasu sha mama nan kusa – A Zango

Ita ma hukumar yansandan jihar ta Kros Ribas ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana mutane 9 sun mace mutu, yayin da sama da mutum 10 suka jikkata.

Bututun iskar gas ta fashe a gidan mai, mutane 9 sun halaka

Gobarar bututun iskar gas

Amma wasu jama’an yankin suna ganin gobarar bata rasa nasaba da fashe fashen bututun mai da ake tsagerun matasa ke yawan yi don satar mai a yankin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kana iya taimakon Buhari idan ya bukata?

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel