Dandalin Kannywood: Rashin lafiya mai tsanani ta kama jaruma Jamila Nagudu

Dandalin Kannywood: Rashin lafiya mai tsanani ta kama jaruma Jamila Nagudu

Yanzu haka labarin da ke zuwa mana na nuni da cewa fitacciyar jarumar nan ta masana'antar Kannywood Jamila Nagudu na kwance a asibiti.

Jarumar wadda cikakken sunan ta shine Jamila Umar an ce tana kwance a wata asibitin kudi ne dake a birnin Kaduna dake a arewacin kasar nan inda take jinyar ciwon da ke damun ta.

Dandalin Kannywood: Rashin lafiya mai tsanani ta kama jaruma Jamila Nagudu
Dandalin Kannywood: Rashin lafiya mai tsanani ta kama jaruma Jamila Nagudu

Legit.ng ta samu labarin cewa fitacciyar jarumar dai ce ta saka hoton nata a bisa kafar sada zumuntar nan na Instagram tana a kwance a gadon asibiti.

Ya zuwa yanzu kuma rahotannin da muka tattaro sun nuna mana cewa jarumar tana fama ne da citar nan ta tsakuwar ciki watau Appendix a turance kuma har ma an yi mata aiki a asibin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel