Kudi ke magana: Real Madrid na shirin sayen Dan wasan Dala Miliyan 180

Kudi ke magana: Real Madrid na shirin sayen Dan wasan Dala Miliyan 180

- Real Madrid ta shiga yarjejeniya da Monaco domin sayen wani Dan wasa

- Dan wasan gaban na Faransa Mbappe zai ci kusan Dalar Euro Miliyan 180

- Idan ta tabbata matashin Dan wasan zai zama mafi tsada a kaf Duniya

Muna samun labari daga Jaridar Marca ta Kasar Sifen cewa Kungiyar Real Madrid ta shiga yarjejeniya da Kungiyar Monaco domin sayen Dan wasan gaban ta Kylian Mbappe.

Kudi ke magan: Real Madrid na shirin sayen Dan wasan Dala Miliyan 180
Real Madrid na shirin sayen Mbappe

Real Madrid ta shirya kashe kudi har Euro Miliyan 180 domin kawo wannan matashin Dan wasa. Idan har cinikin ya tabbata, Dan kwallon zai zama mafi tsada a Duniya sama da irin su Paul Pogba da aka saya Miliyan 105 a kakar bara.

KU KARANTA: Dan wasan kwaikwayo a Ofishin 'Yan Sanda

Kudi ke magan: Real Madrid na shirin sayen Dan wasan Dala Miliyan 180
Dan wasa Mbappe na Kungiyar Monaco

Matashin dai yana cikin wadanda ake yi ganin cewa za su addabi Duniya nan gaba kadan. shiyasa ma dai irin su Kungiyar Chelsea da Manchester City su ka dage wajen ganin sun saye Dan wasan.

Yanzu dai an fi ganin Dan wasan gaban na Faransa zai tafi Real Madrid inda zai rika karbar Dala Miliyan 7 a kowace shekara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wa su ka fi dacewa da albashi mai tsoka?

Asali: Legit.ng

Online view pixel