Ambaliyar ruwa a jihar Gombe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23

Ambaliyar ruwa a jihar Gombe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane 23 ne suka rasa rayukansu sanadiyar ambaliyar ruwa day a afku a jihar Gombe, yayinda gidaje 12 suka halaka.

Shugaban karamar hukumar dake bayar da agajin gaggagwa ta jihar, Mohammed Garba ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa mutane shidda sun mutu a garin Dadinkwa dake Yamaltu-Deba, sannan 16 sun rasu a cikin garin Gombe.

Bayan haka gonaki 119 ne a garin Jauro Baba, Jauro Mai da Jauro Saini dake gundumar Kamo, karamar hukumar Kaltungo suka salwanta sannan kuma an yi hasarar abinci da taki sanadiyyar wannan ambaliya da ya ke ta aukuwa a sassan jihar.

Kayan abincin kuwa da ambaliyar ruwan ya yi awan gaba da sun kai buhuhuna 450 na hatsi a Dadinkowa, sai kuma buhuhuna 11 na takin zamani a karamar hukumar Kaltungo.

Ambaliyar ruwa a jihar Gombe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23
Ambaliyar ruwa a jihar Gombe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23

Ambaliyar ruwan bai bar dabbobi da kayayyakin cikin gida ba.

KU KARANTA KUMA: Karatu ne a gabana ba fim ko aure ba - Aisha Tsamiya

Garba ya ce gwamnatin jahar na cikin shirye shiryen kai kayayyakin tallafi ga mutanen da abun ya shafa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel